Tawagar hadin gwiwa ta Hukumar Kwallon kafa ta Duniya, FIFA da takwararta ta Afirka, CAF, mai gudanar da bincike akan rikicin da ta janyo murabus din shugabancin Hukumar Kwallon kafa ta Najeriya, NFF, ta kammala aikinta na kwanaki biyu, na tattaunawa da masu ruwa da tsaki kuma. ta bar Najeriya 

Wata majiya ta ce jirgin tawagar ya bar Najeriya da misalin karfe 10:00 na dare zuwa Zurich, dake Switzerland, bayan kammala jerin tarurruka da nufin tattara bayanai kai-tsaye da kuma sanin halin da ake ciki sakamakon murabus din mambobin Kwamitin Zartarwa, da babban Sakatare Janar na NFF.

Da isowarsu a ranar Litinin, tawagar ta fara ganawa da Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa (NSC) Shehu Dikko, kafin ta wuce zuwa shelkwatar NFF, inda ta gudanar da dogon taro da manyan jami’ai da ma’aikatan hukumar.

An gabatar da zarge-zarge da dama da suka shafi badakalar kudade da kuma gazawar shugabanci da sauran su yayin tattaunawar, kamar yadda wata majiya ta shaida wa gidan Rediyon Blueprint.

A cewar majiyar, wasu daga cikin zarge-zargen an gabatar da su tare da takardu da rubutattun shaidu da aka mika wa jami’an FIFA da CAF domin tantancewa.

Ana sa ran tawagar za ta yi nazari kan korafe-korafe da bayanan da ta samu daga masu ruwa da tsaki daban-daban kafin ta bayar da shawarwari kan matakin da ya dace a dauka.

Babban abinda kowa yake jira daga Hukumar FIFA da CAF a yanzu shine batun tsarin rikon kwarya mafi dacewa ga Hukumar NFF bayan murabus din shugabancinta.

Yayin taron, an samu saɓanin ra’ayi tsakanin Hukumomin kwallon kafa ta jihohi da Hukumar Wasanni ta Kasa (NSC) game da tsarin da za a dauka na kafa jagorancin rikon kwarya na Hukumar NFF kafin gabatar da zabe.

Wakilin Hukumomin Kwallon kafa ta jihohi a taron, Yakubu Sarma, ya kalubalanci shawarar Hukumar NSC na mika jagorancin rikon kwaryar Hukumar NFF ga wani daga waje.

A cewarsa, abinda ya fi cancanta shine a baiwa mamba dan cikin gida rikon kwaryar jan ragamar Hukumar ta NFF.

Yanzu da tawagar ta koma Zurich, hankali zai koma kan FIFA da CAF yayin da suke nazarin rahotanni, takardu da korafe-korafen da aka mika musu yayin tattaunawar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *