Lionel Messi

Ana sa ran Lionel Messi zai buga wasan bankwana na ƙarshe a ƙasarsa ta Argentina, yayin fafatawa da Benin a wasa sada zumnta a ranar 6 ga Oktobar 2026.

Ɗan wasan wanda ya lashe lambar yabo na Ballon d’Or sau takwas, ya sanar da yin ritaya daga ƙwallon ƙafa ta ƙasa da ƙasa bayan shan kashin da Argentina ta yi a wasan ƙarshe na Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Wasan wanda za a buga a Buenos Aires an mayar da shi wasan bikin murnar kammala aikinsa, inda aka gayyaci dukkan abokan wasansa na tawagar Argentina da suka lashe Gasar Cin Kofin Duniya ta 2022.

An sanya sunan Messi a cikin tawagar koci Lionel Scaloni ne bayan gayyatar da aka tura masa don buga wasan.

Argentina za ta buga wasannin sa da zumunta da ƙasar Bolivia a ranar 30 ga Satumba da kuma Burkina Faso a ranar 3 ga Oktoba.

Sai dai Messi, shi da ‘yan wasan tsakiya Giovani Lo Celso da Rodrigo De Paul, za su buga wasan da Argentina za ta kara da Benin ne kawai.

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Argentina Claudio Tapia, shine ya tabbatar da hakan cikin wani bidiyo da aka fitar a Instagram, inda ya ce an shirya hakanne don Messi “ya samu bankwanar da ya cancanta a ranar 6 ga Oktoba, a nan, a Argentina.”

Messi shi ne ɗan wasan da ya fi ci wa Argentina ƙwallaye da kuma buga mata wasanni, inda ya zura ƙwallaye 125 a wasanni 207 tun bayan fara buga mata wasa a 2005.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *