Gobara ta tashi a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote (ADUSTECH) da ke Wudil, a Jihar Kano, inda ta lalata dukiya da aka kiyasta ta kai ta naira miliyan 20.
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (FFS), reshen Jihar Kano, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba 16 ga Satumbar 2026, inda ta ce jami’anta sun yi gaggawar kai dauki da kuma shawo kan gobarar.
Sanarwar ta ce Hukumar ta karbi kiran gaggawa da misalin karfe 11:38 na safe daga reshen ta kwalejin horon ‘yan sanda ta Wudil, bayan jami’an tsaron jami’ar su ka nemi dauki daga Kwamandan Makarantar.
-
Aikin hanya: Mazauna Karu Sun Yaba Wa Tinubu Da Wike
-
Obasanjo: Da taimakon Najeriya Afirika ta Kudu ta kawo ƙarshen mulkin wariya
-
Messi zai sake buga wa Argentina wasa kafin yin bankwanan ƙarshe
Hukumar ta aike da Jami’anta da take yiwa lakabi da (Green Watch) karkashin jagorancin ASF II, Nura Haladu, domin kaiwa dauki, inda ta gano cewa gobarar ta shafi muhimman takardu da sauran kayayyaki a wani ofis a Sashen koyar da Ilmin tsarin Gine-gine (Architecture).
“A lokacin da suka isa, tawagar ta gano cewa gobarar ta shafi fayil-fayil da sauran kayayyaki a wani ofis dake tsangayar koyar da ilmin Gine-Gine,” in ji hukumar.
Jami’an kashe gobarar na tarayya da hadin gwiwar takwarar su a Jihar Kano, sun yi nasarar kashe wutar, inda aka kiyasta asarar da ta kai kimanin naira miliyan 700.
Hukumar tace dora matsalar gobarar akan “zargin lalacewar wayoyin lantarki,” koda yake a cewar ta kawo yanzu gudanar da cikakken bincike.
Duk da cewa ba safai ake samun matsalolin gobara a manyan makarantun gaba da sakandire a jihar kamar yadda ake samu a manyan kasuwannin ta ba, hadin gwiwar da jami’an hukumar suka yi na nuni da wani sabon shiri da hukumar ke son fitowa dashi wajen tunkarar matsalar tashe-tashen gobara.