Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Jihar Kano ta tsayar da Alhaji Muhammad Sani Abacha, ɗan marigayi tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Janar Sani Abacha, a matsayin ɗan takararta na kujerar gwamnan jihar a zaɓen shekara mai zuwa.
Jam’iyyar ta ce matakin ya biyo bayan janyewar ɗan takarar da aka tsayar tun farko, Muhammad Bello Dalha.
A wani taron faɗaɗa kwamitin zartarwa na jam’iyyar na jihar da aka gudanar a Kano ranar Laraba, shugaban PDP na jihar, Dakta Bello Gambo Bichi, ya ce an gudanar da zaɓen tabbatar da ɗan takarar ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam’iyyar da dokokin zaɓe.
- Majalisar Tarayya ta mika kudirin gyaran kundin tsarin mulki ga majalisun dokokin jihohi
- Najeriya da Faransa na duba yiwuwar sanya jari a harkar yada labarai
- Gobara ta tashi a Jami’ar Aliko Dangote
Ya ce a baya jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fidda gwani inda aka ayyana Muhammad Bello Dalha a matsayin wanda ya yi nasara, sai dai bayan shawarwari tsakanin masu ruwa da tsaki a Kano da Abuja, ɗan takarar ya yanke shawarar janyewa.
Bayan tabbatar da janyewar Dalha, an gudanar da wani sabon zaɓen fidda gwani domin maye gurbinsa, inda aka ayyana Muhammad Abacha a matsayin wanda ya yi nasara.
Shugaban kwamitin zaɓen fidda gwamin, Dakta Abba Abdullahi, ya tabbatar da cewa an gudanar da aikin ne bisa ƙa’idojin jam’iyyar da dokokin zaɓe, tare da tabbatar da cewa Abacha ya cika dukkan sharuddan tsayawa takara.
Rahotanni sun ce Muhammad Abacha ya kasance ɗan takarar jam’iyyar a zaɓukan da suka gabata.
A zaɓen gwamnan Kano na shekarar 2023, Abacha ya zo matsayi na uku da tazara mai yawa, inda ya sha gaban APC, a zaɓen da ɗan takarar New Nigeria People’s Party (NNPP) ya samu nasara.