Ƙasar Saudi Arabia ta yi ƙememen wajen amincewa da buƙatar Najeriya na ƙarin kujerun aikin Hajjin 2027, inda Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya, NAHCON, ta ce rabon kujerun Najeriya zai ci gaba da kasancewa dubu 50.
NAHCON ta ce kujeru dubu 35,000 za su kasance na mahajjatan da hukumomin gwamnati da za su kula da su, yayin da kujeru dubu 15,000 za su kasance na kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi.
Hukumar ta ce Saudi Arabia ta yi bayanin cewa ƙarin kujerun ba zai yiwu ba saboda iyakacin wuraren saukar mahajjata da matsalolin tsarin gine-gine a wuraren ibadar da kuma tsarin bin ƙayyadadden rabon da aka amince da shi ga kowace ƙasa.
- Ta’aziyyar Bamanga Tukur: Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin Tarayya zuwa Yola
- Yadda Najeriya ta cire Ingila a Gasar Cin Kofin Duniya ta mata
- Me ya sa farashin man fetur ke ƙara tashin gwauron Zabi?
Shugaban NAHCON, Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya ce hukumar ta yi amfani da hanyoyin diflomasiyya da na aiki wajen neman ƙarin kujerun, amma ta mutunta matakin ƙarshe da hukumomin Saudi Arabia suka ɗauka.
Ya kuma buƙaci hukumomin jin daɗin mahajjata na jihohi da kamfanonin Hajji masu lasisi su tabbatar da cewa an shigar da bayanan dukkan mahajjatan da ake sa ran za su tafi Hajjin 2027 kafin ranar 26 ga Satumba 2026, yana mai cewa ba za a ƙara wa’adin ba.
Ambasada Yusuf ya ƙara da cewa waɗanda ba su samu gurbin Hajjin 2027 ba za su iya yin rajista domin Hajjin 2028, inda ya bayyana cewa an riga an buɗe tashar rajistar.
