Tawagar Falconets ta Najeriya ta tsallaka zuwa wasan kwata-fainal na Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20, bayan murƙushe Ingila da ci 3-0.

Falconets ta taka rawar gani sosai, inda ta samu nasara ta biyu a gasar kuma ta haɗa jimillar ƙwallaye 13 a wasanni huɗu da ta buga.

Tosin Rafiu ce ta far ci wa Najeriya ƙwallo a minti na 8, kafin Seimeyeha Janet Akekoromowei ta ƙara ta biyu, bayan minti biyu da dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sannan Mary Mamudu ta cikata ƙwallaye na uku a minti na 73 inda hakan ya tabbatarwa Falconets da gagarumar nasara akan Ingila.

Kyaftin ɗin tawagar, Christiana Uzoma, ta taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa Falconets samun nasara yayin da ta kama bugun fanareti na Rachel Maltby domin hana farke ƙwallon da Najeriya ta zura a rabin farko.

A halin yanzu, Falconets ta samu nasara sau biyu, ta yi canjaras ɗaya da kuma rashin nasara ɗaya a gasar, tare da ajiye tarihin buga wasanni biyu ba tare da an zura mata ƙwallo ba.

Najeriya za ta koma fagen fafatawa a wasan kwata-fainal a ranar 20 ga Satumbar 2026.

Falconets za ta kara da ko dai Poland ko kumaColombia a filin wasa na Stadion Miejski ŁKS Łódź da ke Łódź.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *