Wata kotun sasanta rikicin kasuwanci ta ƙasa da ƙasa ƙarƙashin Ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya, ICC, da ke birnin Paris, ta yanke hukunci a kan ƙarar da kamfanin Sunrise Power and Transmission Company ya shigar kan gwamnatin Najeriya.
Kotun ta yanke hukunci a ranar 17 ga Satumba, 2026, inda ta yi watsi da buƙatar kamfanin na neman dala miliyan 680 a matsayin kuɗin sulhu da ruwa, dangane da wani rikici da ya shafi aikin samar da wutar lantarki na Mambila mai ƙarfin megawatt 3,960 a Jihar Taraba.
Kamfanin na kuma neman sama da dala biliyan 2.7 a wani sashe na shari’ar, kan diyya da ruwa da suka shafi ci gaban aikin.
- Saudi Arabia ta ƙi ƙarawa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027
- Ta’aziyyar Bamanga Tukur: Shettima ya jagoranci tawagar gwamnatin Tarayya zuwa Yola
Fadar Shugaban Ƙasa ta ce hukuncin ya kawar da wani babban ƙalubalen shari’a da ya shafe shekaru yana kawo cikas ga aikin tashar samar da wutar lantarkin Mambila.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yaba da aikin Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Prince Lateef Fagbemi, da tawagar Ma’aikatar Shari’a wajen kare muradun Najeriya a shari’ar.
Shugaban ya kuma yaba wa tsoffin shugabannin ƙasa Olusegun Obasanjo da marigayi Muhammadu Buhari, wadanda suka bayar da shaida a shari’ar, tare da sauran shaidu da kwararrun da suka taimaka wajen kare matsayin Najeriya.