Ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah, JIBWIS, ta ce ta tattara jimillar Naira miliyan 189.9 daga kuɗaɗen fatun Layya da rasit a faɗin Najeriya a shekarar 2026.
Shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ne bayyana hakan bayan ya karɓi rahoto daga Kwamitin Tattara Fatun Layya na Ƙasa a wani taro da aka gudanar a Kaduna.
- Kotun ICC ta yi watsi da ƙarar Sunrise kan gwamnatin Najeriya
- Saudi Arabia ta ƙi ƙarawa Najeriya kujerun aikin Hajjin 2027
Rahoton ya nuna cewa kuɗin fatun Layya sun kai Naira miliyan 179.77, yayin da kuɗaɗen rasit suka kai Naira miliyan 10.19, wanda ya kawo jimillar kuɗaɗen zuwa Naira miliyan 189.96.
Jihar Kaduna ce ta fi kowace jiha yawan kuɗin da aka tattara, inda ta samu Naira miliyan 25.86, sai Kebbi da Naira miliyan 25.83, yayin da Sokoto ta zo ta uku da Naira miliyan 19.41.
Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yaba wa kwamitin bisa abin da ya bayyana a matsayin jajircewa da riƙon amana wajen gudanar da aikin, tare da yin addu’ar Allah Ya saka wa masu bayar da gudummawar da alheri.