Brighton ta kawo karshen nasarar Arsenal a gasar Premier League, bayan ta doke zakarun gasar da ci 3-0 a filin na American Express Stadium.

Pascal Groß ne ya fara zura ƙwallo a minti na 31, kafin Charalampos Kostoulas ya ƙara ta biyu a minti na 45. Chema Andrés ya kammala wasan da ƙwallo ta uku a minti na 57.

Arsenal ta shiga wasan ne bayan ta yi nasara a wasanninta huɗu na farko, amma rashin nasarar ta sa wannan cikakkiyar nasarar ta tsaya, yayin da Brighton ta ƙara makinta zuwa 10 bayan wasanni biyar.

Yanzu Arsenal ta na matsayina biyu bayan Man City da maki 12, yayin da Brighton ta ke matsayi na 3 da maki 10 kafin karkare wasan mako na biyar

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *