Majalisar Dokokin Jihar Kano ta tabbatar da nadin tsohon Kakakinta, Balarabe Sa’idu Gani, da mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf, Sunusi Bature Dawakin Tofa, a matsayin kwamishinoni a gwamnatin jihar.
An tabbatar da nadin nasu ne bayan an kammala tantancewa a zaman majalisar na ranar Talata, wanda Kakakin Majalisar, Jibril Isma’il Falgore, ya jagoranta.
- Tinubu ya fara biyan Super Falcons ladan Dala 100,000 bayan lashe WAFCON
- Gwamna Kefas ya gana da rundunar soji a Taraba kan ƙarfafa tsaro
Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya miƙa sunayen mutanen biyu ga majalisar domin tantancewa da amincewa da nadinsu, don cike guraben da ke ma’aikatun albarkatun ma’adinai da yaɗa labarai.
An tabbatar da Balarabe Sa’idu Gani, wanda ya taɓa zama Kakakin Majalisar a lokacin mulkin tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, a matsayin Kwamishinan Ma’aikatar Albarkatun Ma’adinai.
Shi kuwa Sunusi Bature Dawakin Tofa an tabbatar da shi a matsayin Kwamishinan Yaɗa Labarai.
Bayan tantancewar, Bature ya bayyana shirinsa na farfaɗo da kafafen yaɗa labarai mallakar gwamnatin jihar, ciki har da dawo da ayyukan gidan rediyon Kano, faɗaɗa tashoshin ARTV, samar da ƙwararrun ma’aikata da kayan aikin zamani, da kuma farfaɗo da kamfanin buga jaridar The Triumph domin ya koma wallafa jarida kullum.