Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya, NDLEA, ta ce ta kama ƙwayoyin tramadol da sauran miyagun ƙwayoyi na sama da miliyan 1.3, da tabar wiwi ta fiye da kilo 6,000 a wasu samamen da ta gudanar a jihohin Lagos, Edo, Niger, Delta, Ondo, Gombe, Imo da Abuja.

NDLEA ta ce jimillar darajar miyagun ƙwayoyin da aka kama ta haura Naira biliyan 3.4, ciki har da buhunan hodar iblis mai nauyin kilogiram 603.75 da hukumar ta kiyasta darajarsu ta kai sama da Naira biliyan 1.8.

A Delta, jami’an hukumar sun kama wani mutum mai shekaru 49, wanda ake zargi da kwaikwayon babban jami’in ’yan sanda domin tsallake shingen binciken ababen hawa yayin safarar miyagun ƙwayoyi. An kama shi da kilogiram 292.48 na tabar wiwi, tare da wani da ake zargi da haɗin gwiwarsa

A Niger kuma, jami’an NDLEA sun kama matasa uku masu shekaru 18 zuwa 20 da bindigogin AK-47 guda biyu da aka ƙera a cikin gida da bindiga kirar gida guda ɗaya da harsasai tara.

A wani samamen daban a hanyar Abaji zuwa Abuja, an kama wasu mutane biyu da fiye da ƙwayoyin tramadol miliyan 1.1 da wasu miyagun ƙwayoyi.

A Lagos, jami’an NDLEA sun kama mutane da dama tare da tramadol da tabar wiwi da kuma kusan kilogiram 998 na iskar nitrous oxide.

A Gombe kuwa, an kama mutane biyu da capsules tramadol 154,480.

A Ondo, jami’an hukumar sun lalata gonar tabar wiwi mai girman hekta biyu, inda suka ce an lalata kusan kilogiram 5,000 na tabar wiwi tare da kama mutane huɗu.

A Imo kuma, an kama wani mutum da kilogiram 43.85 na tabar wiwi.

Shugaban NDLEA, Brig. Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya yaba wa jami’an hukumar kan ayyukan, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da amfani da bayanan sirri da kuma hanyoyin da suka dace wajen yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *