Kungiyoyin ‘ƴan bindiga bakwai a Habasha sun kafa ƙawance domin kalubalantar gwamnatin tarayya, kamar yadda wani jami’in kungiyar Tigray People’s Liberation Front (TPLF) ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP a ranar Lahadi.
Kungiyoyin sun hada da dakarun Tigray, da mayakan Fano masu kishin ƙabilar Amhara da kuma Oromo Liberation Army (OLA), wadda ke gudanar da wani bore da makamai a yankin Oromia, mafi yawan jama’a a ƙasar, tare da wasu kungiyoyi hudu.
- Uganda ta dakatar da haɗin gwiwar soji da Turkiyya sakamakon rikicin siyasa
- An kashe mutum biyu a harin da Ukraine ta kai Moscow – Rasha
- Babu yiwuwar AI ta jawo ƙarshen duniya a 2030-Jensen Huang
Mataimakin shugaban TPLF, Amanuel Assefa, ya ce an kafa ƙawancen ne domin kawar da gwamnatin da ke mulki da kuma taimakawa wajen kafa gwamnatin rikon kwarya.
Ya ce kungiyoyin sun shafe sama da shekara guda suna tattaunawa kan yadda za su hada kai, yana mai cewa suna da yakinin cewa za su samu nasara.
Ya kuma bayyana cewa shugaban kungiyar Fano, Zemene Kasse, ne zai jagoranci ƙawancen.
A halin yanzu, gwamnatin Habasha da TPLF sun tara sojoji a kan iyakar jihar Tigray da ke arewacin ƙasar a cikin ‘yan watannin nan, lamarin da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta ce ya kara tayar da fargabar sake barkewar yakin da ya yi sanadin mutuwar kimanin mutane 600,000.