Tawagar ‘yan mata ‘yan ƙasa da shekaru 17 ta Najeriya, Flamingos, ta ci gaba da taka rawar gani a Gasar WAFU B U17 ta 2026 inda ta samu nasarar doke Burkina Faso da ci 2-0 a filin wasa na Charles Konan Banny da ke Yamoussoukro a ranar Litinin.
A yayin rabin lokaci na farko mai cike da gwagwarmaya, tawagun biyu sun kasa zura ƙwallo a raga duk da damammaki masu kyau da suka samu.
Flamingos, wadda ta kammala a matsayi na biyu lokacin da aka fara gasar a ƙasar Ghana shekaru biyu da suka gabata, ita ta mamaye mallakar ƙwallo da kuma matsa lamba amma ba ta iya amfani da damarta ba, yayin da masu tsaron gidan Burkina Faso suka jajirce wajen tsaron gidansu.
Bayan samun turjiya a rabin farko, yayin rabi na biyu Najeriya ta ƙara kaimi wajen neman nasara.
-
Falconets ta yi ban kwana da Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ‘yan ƙasa da shekaru 20
-
Ƙwallaye uku da Raphinha ya zura sun baiwa Barcelona nasarar ci 3-1 a kan Sevilla
-
Salah ya zura ƙwallaye uku, yayin da Trabzonspor ta ragargaji Galatasaray
An karya alƙadarin Burkina Faso a ƙarshe a minti na 82 lokacin da Mary Dunstan ta zura wani ƙwallo mai kyau a raga.
Najeriya ta ƙara ƙwallonta na biyu a cikin ƙarin lokaci yayin da Oluwakemi Adegbuyi ta ci ƙwallo don tabbatar da nasarar Flamingos yayin karawar.
Da wannan nasara na ci 2-0, a yanzu, Flamingos ta ci gaba da zama a saman tebur da maki tara cikakke daga wasanni uku, inda take ci gaba da tafiya ba tare da shan kaye ba a gasar.