Shugaban kamfanin Nvidia, Jensen Huang, ya yi watsi da fargabar cewa fasahar basirar ɗan Adam, wato AI, za ta iya jawo halakar bil’adama nan da shekarar 2030, yana mai cewa akwai “kashi sifili cikin ɗari” na yiwuwar duniya ta ƙare sakamakon AI.

Da yake magana da shirin Sunday Morning na CBS News, Huang ya goyi bayan ra’ayin Shugaban Amurka Donald Trump cewa damuwar da ake nunawa game da illolin AI ba ta da tushe.

Huang ya ce ya kamata masana’antar AI ta ci gaba da haɓaka fasahar cikin sauri, tare da tabbatar da cewa kayayyakin da ake samarwa suna da aminci.

Ya ce: “Ya kamata mu tafi da sauri gwargwadon yadda za mu iya, ba tare da la’akari da kowa ba. Za mu tafi da sauri gwargwadon yadda za mu iya, amma ba za mu taɓa fitar da kayayyaki kafin su kasance a shirye ba, kuma bai kamata mu fitar da kayayyakin da ba su da aminci ba.”

Muhawarar da ake yi kan haɗarin AI ta ƙara ƙamari bayan Shugaban kamfanin Anthropic, Dario Amodei, ya yi kira da a rage saurin haɓaka sabbin nau’ukan AI.

Ra’ayoyin Huang sun ƙara bayyana rarrabuwar da ke tsakanin masu ruwa da tsaki a masana’antar AI game da yadda ya kamata a tafiyar da ci gaban fasahar.

Yayin da Huang ke goyon bayan ci gaba cikin sauri tare da ɗaukar matakan tabbatar da tsaro, shugaban kamfanin AI na Anthropic Dario Amodei ya yi gargadin cewa tsarin AI na iya fara inganta sabbin nau’ukan fasahar cikin sauri fiye da yadda mutane za su iya fahimta ko sarrafa su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *