Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kwamitin shirye-shiryen tunawa da bikin cika shekaru 66 da samun ‘yancin kan Najeriya, tare da mai da hankali kan yin tunani a kan kyawawan gadon da iyayen ƙasa suka bari a baya.
Shugaban Sashen Bayanai da hulda da Jama’a a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Chris Ugwuegbulam, wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an ƙaddamar da kwamitin ne a ranar Alhamis a Abuja.
Da yake jawabi a wurin taron ƙaddamar da kwamitin a Abuja, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) kuma shugaban kwamitin, Sanata George Akume, ya jaddada muhimmancin murnar gudunmawa, sadaukarwa, da kuma kyakkyawan gadon da iyayen ƙasa da jaruman da suka yi yaƙin ‘yancin kan Najeriya daga mulkin mallaka suka bari a baya.
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dagacin kauye a Kano
- FCT: ’Yan sandan sun kama mutum 300 a samamen maboyar masu laifi
SGF, wanda Babban Sakatare na Ofishin Al’amuran Siyasa da Tattalin Arziki (PEAO), Aftare Mrs. Bekearedebo Augusta Warrens ta wakilta a wurin taron, ya ce nasarorin da Najeriya ta samu tun bayan samun ‘yancin kai an gina su ne a kan tushen da ‘yan kishin ƙasar suka shimfiɗa.
Ya jaddada muhimmancin tunawa da sadaukarwar da suka yi yayin da ake bincike da tunani kan tafiyar ƙasar tun daga ranar 1 ga Oktoba, 1960.
Ya ce, wannan taro zai kuma ba gwamnati mai ci damar baje kolin nasarorin da ta samu da kuma fito da ƙoƙarin da ake yi na sake gyara ƙasar ta hanyar tsare-tsaren gyara, a tsakiyar kalubalen zamantakewa da tattalin arziki da ƙasar ke fuskanta.
Ya jaddada cewa al’amuran bikin na wannan shekara za a gudanar da su ne ba tare da kashe ɗumbin kuɗaɗe ko hayaniya ba, yayin da ya ƙarfafa mambobin kwamitin da su yi aiki cikin hanzari saboda ƙarancin lokacin da ya rage kafin ranar 1 ga Oktoba.
A cewarsa, tsarin shirye-shiryen zai faro ne da Taron Manema Labarai na Duniya a ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026; addu’o’i ranar Juma’a, 25 ga Satumba; da ibadar Ikilisiya a ranar Lahadi, 27 ga Satumba, 2026; Lakcar Bikin Ranar ‘Yancin Kai a ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026, da kuma jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ƙasa baki ɗaya a ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, 2026.
Kwamitin ya ƙunshi SGF a matsayin shugaba tare da mambobi masu zuwa: Ministan Ƙudi kuma Ministan Daidaita Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele; Ministan Bayanai da Wayar da Kan Ƙasa, Mohammed Idris; Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo; Ministan Harkokin Waje, Amb. Bianca Odumegwu-Ojukwu; Ministan Tarayyar Abuja (FCT), Barr. Nyesom Wike; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsara Tattalin Arziki, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, CON; Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaron Ƙasa, Mallam Nuhu Ribadu; Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Haɗin Kan Manufofi, Hadiza Bala Usman; da Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Bayanai da Dabarun Sadarwa, Mista Bayo Onanuga.
Kwamitin ya kuma haɗa da Babban Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Kafofin Yada Labarai da Sadarwar Jama’a, Chief Sunday Dare; Babban Sakatare na Fadar Shugaban Ƙasa (State House), Engr. Temitope Peter Fashedemi; Babban Sakatare na Ofishin Ayyukan Gaba Ɗaya (GSO), Dr. Ibrahim Abubakar Kana; Babban Sakatare na Ma’aikatar Kiwon Lafiya ta Tarayya, Ms. Kachollom Daju, mni; Babban Sakatare na Ofishin Al’amuran Majalisar Gudanarwa (CAO), Dr. John Chidiebere Ezeamama; Inspector-General na ‘Yan Sanda, Mista Olatunji Disu; Darakta Janar na Hukumar Tsaron Cikin Gida (DSS), Mista Adeola Oluwatosin Ajayi; Kwamandan Rundunar Tsaron Fadar Shugaban Ƙasa (Guards Brigade), Brig.-Gen. Adebisi Olusegun Onasanya; da Babban Sakatare na Ofishin Al’amuran Siyasa da Tattalin Arziki (PEAO), Mrs. Bekearedebo Augusta Warrens.