Shugaban Majalisar Dokokin Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce Iran na da ikon kai hare-haren makamai masu linzami a duk inda ta ga dama, ba tare da wani takunkumi ba.
- Malami ya ce rikicin Mambilla ya fara tun kafin ya zama minista
- Hukuncin kotu kan Magu ya sake buɗe batun ikon Majalisa da bin doka
Ghalibaf, wanda kuma shi ne babban mai shiga tsakani na Iran a tattaunawar da take yi da Amurka, ya ce ƙasarsa ba za ta mika wuya ko ta dakatar da harkokinta ba duk da rikicin tattalin arziki, soja da diflomasiyya da take fuskanta.
Ya ce Iran za ta ci gaba da mayar da martani da ƙarfi, yana mai cewa hakan shi ne abin da ta ke yi tun farko kuma ya sanya abokan hamayyarta cikin mawuyacin hali.