Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce rikicin da ya shafi kamfanin Sunrise Power da aikin wutar lantarkin Mambilla ya fara tun shekarar 2003, shekaru kafin ya zama Ministan Shari’a.

Ofishinsa ya ce Malami ya gaji tsohuwar takaddamar ne da ta riga ta shafi gwamnatoci da jami’ai daban-daban, kuma rawarsa ita ce bai wa gwamnatin tarayya shawarar shari’a kan yadda za ta magance rikicin.

Sanarwar ta ce tsohon Shugaba Muhammadu Buhari bai amince da biyan dala miliyan 200 da aka tattauna a matsayin yarjejeniyar sulhu ba, sannan Malami ya umurci lauyoyin gwamnati su yi adawa da yunƙurin Sunrise na aiwatar da yarjejeniyar.

Malami ya kuma musanta zargin cewa ya shiga wata yarjejeniyar cin hanci, yana mai cewa zai fitar da cikakken martani bayan nazarin hukuncin kotun sulhu mai shafuka 616.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *