Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ya ayyana tsawaita wa’adin Ibrahim Magu a matsayin mukaddashin shugaban Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ba bisa doka ba, ya sake buɗe muhawara kan muhimmancin bin tsarin da doka ta tanada wajen naɗe shugabannin manyan hukumomin gwamnati.
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta soke wani hukuncin Babbar Kotun Tarayya na shekarar 2019, wanda ya amince da Magu ya ci gaba da riƙe mukaddashin shugaban EFCC, duk da cewa Majalisar Dattawa ta ƙi tabbatar da naɗinsa a matsayin cikakken shugaban hukumar sau biyu.
Magu ya riƙe mukaddashin shugabancin EFCC daga shekarar 2015 zuwa Yuli 2020, lokacin da aka dakatar da shi daga mukamin.
- Shugabannin Gulf za su matsa wa Trump kan hanyar kawo ƙarshen rikicin Gabas ta Tsakiya
- An buɗe taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 a New York
Shari’ar da ta kai ga wannan sabon hukuncin ta samo asali ne daga ƙarar wani lauya, Johnmary Jideobi, wanda ya kalubalanci Magu da ci gaba da riƙe mukamin bayan Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da naɗinsa sau biyu.
Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya ce hukuncin ya tabbatar da matsayin da Majalisar ta ɗauka a shekarun 2016 da 2017.
A cewar Saraki, Majalisar ta ƙi tabbatar da Magu ne saboda tana ganin dole ne a bi abin da doka ta tanada, duk da zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa.
Saraki ya ce shi da wasu ’yan majalisa da iyalansu sun fuskanci tsangwama saboda wannan matsaya, amma ya bayyana hukuncin kotun a matsayin abin da ya tabbatar da cewa tsayawa kan abin da mutum ya yi imanin cewa shi ne daidai na iya ɗaukar lokaci kafin a samu sakamakonsa.
Hukuncin ya jawo hankali kan yadda za a tafiyar da mukaddashin shugabancin hukumomin da doka ta tanadi tsarin tabbatar da shugabanninsu, musamman batun ko mutum zai iya ci gaba da riƙe irin wannan mukami na dogon lokaci bayan an ƙi tabbatar da naɗinsa.