Jam’iyyar NDC ta ce ta kammala shirye-shiryen kafawa da ƙaddamar da Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa, wadda za ta jagoranci shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027.

Jam’iyyar ta ce ɗan takararta, Peter Obi, da abokin takararsa, Rabiu Musa Kwankwaso, sun gudanar da tattaunawa da shugabannin jam’iyyar kan tsarin majalisar, kuma an ba su damar zaɓar wasu daga cikin manyan jami’an yaƙin neman zaɓen tare da tuntuɓar jam’iyyar.

NDC ta ce an riga an kammala tsarin majalisar tun watan Agusta, yayin da ake jiran shawarwari daga Obi da Kwankwaso kafin a sanar da sunayen jami’an tare da ƙaddamar da majalisar.

Jam’iyyar ta ce an kuma shirya jadawalin yaƙin neman zaɓen, amma ana kan kammala shirye-shiryen tattara kuɗaɗen yaƙin neman zaɓen.

Game da gudanar da kuɗaɗen, jam’iyyar ta ce Daraktan Kuɗi da mataimakinsa, tare da Ma’ajin jam’iyyar na Ƙasa, za su kula da asusun yaƙin neman zaɓen cikin gaskiya da rikon amana, domin cika buƙatun da dokar zaɓe ta tanada.

NDC ta kuma umarci shugabannin jam’iyya na jihohi da ƙananan hukumomi su fara tattara sunayen jami’an da za su wakilci jam’iyyar a rumfunan zaɓe, tare da kammala aikin cikin makonni biyu kafin fara horas da jami’an.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and Digital Manager at Blueprint Radio Hausa. He holds a B.Sc. and a Diploma in Mass Communication. He has experience in news reporting, radio production, digital media management, and content creation.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *