Sanata Tony Nwoye na jam'iyyar ADC ya hau kujerar shugaban marasa rinjaye a zauren majalisar dattawa.

Yayin da manyan zabubbukan 2027 suke matsowa a Najeriya, ana ci gaba da fuskantar wani babban sauyi a taswirar siyasar kasar, musamman a cikin kwanakin nan da guguwar sauyin ke shafar zauren majalisar kasar.

A zaman Majalisar Dattawa na ranar Laraba PDP, wadda a da ita ce babbar jam’iyyar adawa, ta ci gaba da rasa mambobinsa, lamarin da ya bai wa jam’iyya mai mulki APC damar kara mamaye zauren Majalisar.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta wasikun sauya sheka na sanatoci biyu da suka fice daga PDP da kuma guda daya daga SDP zuwa APC.

Sanatocin sun hadar da tsohon Shugaban Marasa Rinjaye Sanata Osita Ngwu mai wakiltar Enugu ta Yamma, da Sanata Anthony Siyako Yaro na Gombe ta Kudu.

Sai kuma dan majalisa mai wakiltar Nassarawa ta Yamma, Sanata Aliyu Wadada.

Dukkanin su sun bayyana rikice-rikicen cikin gida da tsofaffin jam’iyyunsu ke fama da su a matsayin babban dalilin ficewarsu, suna masu cewa sun koma APC ne domin mara wa shirye-shiryen raya kasa na Gwamnatin Tarayya baya.

A bangare guda, ficewar ta su ta haifar da gurbi a shugabancin marasa rinjaye wanda nan take majalisar ta nada Sanata Tony Nwoye na jam’iyyar ADC a matsayin sabon shugaba, mukamin da ya subuce daga hannun babbar jam iyyar adawa ta PDP a karon farko cikin shekaru 16 da komawar kasar mulkin APC.

A halin yanzu, jam’iyyar APC tana da 87 daga cikin mambobi 109, lamarin da ke nuna cewa tana da ikon zartar da kowane irin kuduri ko amincewa da nade-naden shugaban kasa ba tare da fuskantar turjiya mai karfi ba.

Masu lura da al’amuran yau da kullum na ganin cewa wannan guguwar sauya sheka na nuna yadda jam’iyyar PDP ke kara raunata, yayin da ake tunkarar babban zaben 2027. Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke kokarin dinke barakar da ke tsakanin manyan jiga-jiganta, da yanzu haka suke gaban kotun koli.

A ranar laraba ne kotun koli ta ajiye hukuncin karshe na karar da PDP ta shigar sai wani lokaci nan gaba, domin yanke hukuncin karshe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *