Gobara ta ƙona shaguna da dukiyoyin miliyoyin naira a kasuwar sayar da kayan gini a Eda Plaza, da ke Jabi, a Abuja.
Cikin wani faifen bidiyo da gidan talabijin na NTA, ya wallafa, an ga masu shagunan da lamarin ya rutsa da su suna ƙoƙarin tseratar da sauran kayan su.
Wani mashaidin gani da ido wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce wani daga kasuwar ne ya sanar wa surukinsa wanda ya ke da shaguna a kasuwar cewa gobarar ta tashi ne da misalin karfe 3:00 na safe.
“Da misalin karfe 3:00 na safe muna gida, sai surukina ya samu kira daga wani abokin aiki anan plaza din cewa gobara ta tashi. Nan da nan muka hanzarta zuwa can. Da muka isa, mu ka ga lamarin ya tsananta sosai,” in ji shaidan.
Ya ƙara da cewa, da suka isa wurin, gobarar ta riga ta bazu sosai, kuma ɗaya daga cikin shaguna biyu na surukin na sa ne kawai bai kama da wuta ba.
“A cikin wannan plaza, surukina yana da shaguna biyu da kuma wajen ajiyan kaya. Abin takaici, ɗaya daga cikin shagunan ne kawai ya rage. Shago ɗaya da wajen ajiyar duk sun ƙone gaba ɗaya,” in ji shi.
Mashaidin ya bayyana cewa darajar kayan da suka ƙone ya kai sama da Naira miliyan 20, sannan ya koka da cewa wasu daga cikin kayan da suka ƙone an kawo su ne daren da ya gabata kafin faruwar lamarin.
Kazalika, ya ce ba a samu rasa rayuwaka ba yayin gobarar.
Da Gidan Rediyon Blueprint ya tuntuɓi Ma’aikatar Kashe Gobara ta Birnin Tarayya, Abuja, domin jin sanadin tashin gobarar, hukumar ba ta ce komai ba tukuna.
Sai dai ta yi alkawarin sake kira ta sanar da wakilin mu kan musabbabin tashin gobarar.