Gabriel Jesus, dan wasan gaba na Brazil da Arsenal

Ƙungiyar Barcelona ta cimma yarjejeniya da Arsenal kan sayan dan wasan gaba na Brazil, Gabriel Jesus, a cewar wani rahoto.

Masanin harkokin saye da sayarwa na ‘yan wasa, Fabrizio Romano, ne ya sanar da hakan a shafinsa na X a ranar Lahadi.

Romano ya ce Barcelona za ta biya kuɗi Yuro miliyan 10 tare da wasu ƙarin ƙudi, domin sayen ɗan wasan gaban mai shekaru 29.

Ya ƙara da cewa an tsara wa Jesus tafiya zuwa ƙasar Spaniya da zarar Arsenal ta ba shi damar tafiya.

Romano ya rubuta: “Gabriel Jesus da Barcelona, an cimma yarjejeniya har zuwa watan Yunin 2028 tare da zaɓin ƙara shekara ɗaya, da kuma kuɗin da ya wuce Yuro miliyan 10 da za a biya Arsenal.

“Yarjejeniyar ta kuma haɗa da zaɓin ƙara shekara guda, har zuwa 2029.

“Gabriel ya amince da tayin Barcelona nan take, saboda yana ganin damar da ya daɗe yana mafarkinta.”

“Arsenal ta ba shi izinin tafiya a ranar Litinin.”

Wannan yarjejeniya ta zo ne a matsayin mafita ta ƙarshe ga kocin Barcelona, Hansi Flick, wanda ke neman ɗan wasan gaba tun bayan tafiyar Robert Lewandowski da kuma Ferran Torres.

Barcelona ta kuma yi ƙoƙarin sayen Julián Álvarez na Atlético Madrid, amma Atlético ta ce ɗan wasan ba na sayarwa ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *