'Yan wasan Flamingos yayin atisaye

Za a buɗe sansanin tawagar ‘yan matan Najeriya masu shekaru ƙasa da 17, wato Flamingos, a ranar Lahadi, a Abuja, yayin da kocin tawagar, Hakeem Busari, zai fara shiga mataki na ƙarshe na shirye-shiryen zuwa Gasar Cin Kofin Duniya ta ’yan ƙasa da shekaru 17 na mata da za a buga a Marokko.

’Yan wasa 26 ne za su halarci sansanin da ke Serob Legacy Hotel da ke Wuye, Abuja.

Ana sa ran za su fara atisaye da ƙarfi ranar Litinin mai zuwa, yayin da kocin zai fara sanar da su dabarun da za suyi amfani da su yayin gasar wanda zai gudana daga 17 ga watan Oktoba zuwa 7 ga watan Nuwamba.

‘Yan wasan da Busari ya gayyata zuwa sansanin a Abuja gabanin wannan babban baje kolin na duniya sun haɗa da:

Masu tsaron raga uku:5Ifesinachi Iloh daga kungiyar (Solo Wonders), Mercy Felix (Obosa FA) da Precious John (Pelican Stars).

Masu tsaron gida takwas:

Elizabeth Adesuyi (Pacesetter Queens), Esther Stephen (Unification Ladies), Chidera Oparanmegwa (Bayelsa Queens), Azeezat Oduntan (Robo Queens), Opeyemi Sunday (Nasarawa Amazons), Omelogu Precious (Tophat SC), Christiana Ogunbunmi (Soccer Talent FC) da Taiwo Abdulazeez (Dannaz Ladies).

‘Yan wasan tsakiya takwas:

Kaosarat Akanji (Dreamstar Ladies), Awawu Bashiru (Confluence Queens), Mary Dustan (Bayelsa Queens), Muinat Rotimi (Nakamura FA), Kate Laniran (Espora Queens), Annabelle Olubajo (Savannah United), Grace Akingboye (Ghetto Tigers) da Eniola Abdulquadri (Unstoppable FA).

‘Yan wasan gaba shida:

Adebimpe Kashimawo (Asisat Oshoala FA), Harmony Chidi (Bayelsa Queens), Mmesoma Uchendu (Ibom Angels), Istifanus Shavi (Youth Arise FA), Shakirat Sarafa (Remo Stars Ladies) da Chisom Chukwuemeka (Diamond Stars).

Idan za a iya tunawa, Flamingos ne suka doke Jamhuriyar Benin gida da waje a zagayen ƙarshe na neman tikitin shiga gasar, inda suka tabbatar da halartar gasar ta duniya.

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA, ta fara gudanar da wannan gasa ne a New Zealand a 2008, kuma Najeriya ta halarci dukkanin su sai dai ban da na 2018 da aka yi a Uruguay.

Gasar Cin Kofin Duniya ta ’yan ƙasa da shekaru 17 na mata wanda za ayi a bana za ta kasance ta 10, kuma za a gudanar da ita a Marokko daga 17 ga Oktoba zuwa 7 ga Nuwamba.

Zakarun da ke riƙe da kofin a yanzu ita ce Koriya ta Arewa, wadda ta lashe kofin karo na 4 a tarihin gasar a 2025.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *