A yayin da aka fara Gasar Ƙwararrun Ƙwallon Ƙafa ta Firimiyar Najeriya, (NPFL) a ranar Jumma’a, 28 ga watan Agustan 2026, inda Shooting Stars ta doke Inter Lagos FC da ci 2-1, masoya da kuma masu nazarin wasannin ƙwallon ƙafa na ci gaba da tafka muhawara akan wanda za ta lashe Gasar kakar bana ta 2026/27.
Ko zakarar da ke riƙe da kofin, Enugu Rangers, za ta iya kare kambun da ta lashe a bara; ko kuma za a samu sabon zakara?
Rangers dai ta lashe Gasar NPFL a karo na tara kenan a bara bayan ta doke Ikorodu City da ci 2-1 a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke Onikan, Jihar Legas.
-
Liverpool ta cimma yarjejeniyar fam miliyan 123 don sayan Bradley Barcola daga PSG
-
Premier League: Abubuwan da za a sa ido a mako na 2
-
Liverpool ta sake tashi 2–2, Forest ta hana Iraola samun nasara a Anfield
Rangers, wanda ake mata laƙabi da Flying Antelopes, ita ce kawai ƙungiyar da ba ta taɓa faɗawa gurbin gajiyayyu daga gasar Firimiya ta Najeriya ba.
Har ila yau, Rangers ta lashe Gasar Super Six ta NPFL ta 2026 da aka gudanar a Jos, jihar Filato bayan ta doke mai masauƙin baƙi, Plateau United da ci 1-0 a wasan ƙarshe da aka buga a sabon filin wasa na Jos.
Rangers za ta fara kare kambunta ne da karawa da Katsina United a gida a ranar Lahadi, 30 ga watan Augustan 2026 da misalin karfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.
Ga jadawalin sauran wasannin da za buga a ranar Lahadi, 30 ga watan Augustan 2026:
Abia Warriors za ta kara da Kun Khalifat FC
Barau za ta karɓi baƙuncin Nasarawa United
Niger Tornadoes za ta kece raini da Enyimba
Rivers United za ta kara da Plateau United
Enugu Rangers za ta kara da Katsina United
Ikorodu City da Ranchers Bees
Bendel Insurance za ta kece raini da Warri Wolves FC
Doma United da Sporting Lagos FC
Kwara United za ta kara da Kano Pillars
Za a buga waɗannan wasannin ne da misalin ƙarfe 4:00 na yamma agogon Najeriya.
Ku turo mana da ra’ayoyinku a sashen kwamen akan ko wa ku ke ganin za ta lashe Gasar NPFL ta bana 2026/27?
