Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci a yi garambawul ga tsarin shari’ar Najeriya domin hana masu hannu da shuni amfani da guraben da ke cikin dokoki da dabarun gurfanarwa wajen kauce wa hukunci.
Shettima ya bayyana hakan ne a Abuja, lokacin da ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron horas da alƙalai da manyan alƙalai na shekara-shekara, wanda Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) da Cibiyar Horar da Alƙalai ta Ƙasa (NJI) suka shirya.
- Rundunar ’yan sandan FCT ta gana da babban jami’in rundunar sojin Najeriya
- EFCC da ’yan sandan Koriya ta Kudu sun fara horas da jami’ai kan binciken kuɗaɗen haram da na intanet
A saƙon da ya isar a madadin shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasar ya buƙaci bangaren shari’a da ya kawar da matsalolin da ke cikin tsarin gudanar da shari’a waɗanda ke ba wa wasu damar tsere wa hukunci.
Ya ce akwai buƙatar a sake fasalin tsarin shari’ar sosai domin tabbatar da cewa babu wani mutum da zai yi amfani da matsayinsa ko alaƙarsa da masu iko wajen karkatar da dokoki domin guje wa hukuncin da ya dace da shi.
Shettima ya jaddada cewa ya kamata a tabbatar da cikakken aiwatar da doka ba tare da la’akari da matsayin mutum ko ƙarfin ikonsa ba.