Shugabannin kwamitocin kula da rundunar sojin saman Najeriya na Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun kai ziyarar ta’aziyya ga Babban Hafsan Sojin Sama, Air Marshal Sunday Kelvin Aneke, bayan hatsarin jirgin sama da ya shafi jami’an rundunar.

Sanarwar ta ce Sanata Osita Ngwu da ɗan majalisa Kabiru Rurum, waɗanda ke jagorantar kwamitocin a majalisun biyu, sun kai ziyarar tare a hedikwatar rundunar sojin sama da ke Abuja ranar 13 ga Oktoba, 2026.

A yayin ziyarar, ’yan majalisar sun miƙa saƙon ta’aziyyarsu ga babban hafsan sojin sama, jami’an da abin ya shafa da kuma sauran al’ummar rundunar, tare da jajantawa iyalan waɗanda suka gamu da wannan ibtila’i.

Sun yaba da sadaukarwar jami’an sojin sama wajen yi wa ƙasa hidima, tare da tabbatar wa rundunar cewa Majalisar Tarayya za ta ci gaba da ba ta goyon baya a wannan lokaci mai wuya.

Haka kuma, sun yi addu’ar Allah Ya ba waɗanda abin ya shafa da iyalansu haƙuri, ƙarfi da kwanciyar hankali, tare da roƙon Allah Ya kiyaye sauran jami’an rundunar daga irin wannan ibtila’i.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *