Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya halarci gangamin siyasa na nuna goyon baya ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da ɗan takarar gwamnan Legas na jam’iyyar APC, Dr. Obafemi Hamzat, tare da mataimakiyarsa, Princess Damilola Sonayon James.
An gudanar da gangamin ne a filin wasa na Mobolaji Johnson Arena da ke Onikan, Legas, inda Sanwo-Olu ya ce taron ya ba su damar kusantar al’ummar jihar tare da sake jaddada aniyarsu ta ci gaban Legas da Najeriya.
- Majalisar Tarayya ta nuna goyon baya ga rundunar sojin sama bayan hatsarin jirgi
- Shettima ya buƙaci gyara tsarin shari’a domin hana masu hannu da shuni kauce wa hukunci
A cikin saƙon da ya wallafa, gwamnan ya gode wa waɗanda suka halarci gangamin domin nuna goyon bayansu, yana mai cewa gwamnatinsa na lura da buƙatun jama’a kuma ba za ta ɗauki goyon bayansu da wasa ba.
Sanwo-Olu ya ƙara da cewa za su ci gaba da ƙoƙarin aiwatar da ayyukan da za su amfanar da al’ummar Legas.