Kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa ta jam’iyyar African Democratic Congress (ADC-PCC) ta yi Allah-wadai da ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Abuja, tana zargin hakan da yunƙurin raunana dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama a Najeriya.

Daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na kwamitin ADC-PCC, Kola Ologbondiyan, ya bayyana hakan ne yayin mayar da martani kan bikin ƙaddamar da kwamitin a ranar Laraba.

Ya zargi APC da matsa wa gwamnonin jam’iyyun adawa lamba domin su shiga cikinta ko kuma a saka su cikin kwamitin yaƙin neman zaɓenta.

Ologbondiyan ya kuma zargi gwamnatin APC da amfani da hukumomin gwamnati, jami’an tsaro da ɓangaren shari’a wajen raunana jam’iyyun adawa.

Ya bayyana cewa ’yan Najeriya na fuskantar matsin tattalin arziki, yunwa da rashin tsaro, yana mai zargin cewa shugabannin da ke mulki sun fi mayar da hankali kan yadda za su ci gaba da riƙe madafun iko maimakon magance matsalolin jama’a.

Kakakin kwamitin ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa na tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, na da gogewa da ƙwarewar siyasa da za su taimaka wajen dawo da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya.

Ya bayyana Atiku a matsayin ɗan siyasa mai gogewa da haɗin kai a faɗin ƙasa, wanda a cewarsa zai iya taimakawa wajen haɗa kan Najeriya da farfaɗo da cibiyoyin dimokuraɗiyya.

ADC-PCC ta yi kira ga ’yan Najeriya, kafafen yaɗa labarai, ƙungiyoyin fararen hula da ƙasashen duniya da su goyi bayan matakan kare tsarin dimokuraɗiyyar jam’iyyu da dama.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *