Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mutum tare da ƙaddamar da neman wani da ake zargi da sare wa wani matashi wuyan hannu yayin wani rikicin siyasa a cikin birnin Bauchi.
A cikin sanarwar da kakakin rundunar, SP Nafiu Habib, ya fitar a ranar 14 ga Oktoba, 2026, ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:30 na safe tsakanin wasu mutane biyu a yankin Bakin Kura.
Sanarwar ta ce a yayin rikicin, wani mutun, wanda ake zargin abokin wani ne, ya fito da adda tare da sare wa matashin wuyan hannu, lamarin da ya sa ya faɗi kuma ya suma.
- RMAFC ta buƙaci ma’aikata su ƙara ƙwazo da riƙon amana
- INEC ta ce fasahar AI ba ita ce za ta yanke sakamakon zaɓen 2027 ba
- Masana sun bukaci a yi amfani da fasaha AI cikin gaskiya wajen zaɓen 2027
An garzaya da wanda abin ya shafa zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi, inda yake karɓar magani kuma yana samun sauƙi.
’Yan sandan sun ce an kama wani matashi, wanda ke taimakawa wajen bincike, yayin dayan ya tsere. Rundunar ta ce ana ƙoƙarin gano inda yake domin kama shi.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Sani-Omolori Aliyu, ya yi Allah-wadai da duk wani nau’in rikicin siyasa da ta’addancin ’yan daba, yana mai gargaɗin cewa rundunar ba za ta lamunci duk wani abu da zai kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron jama’a ba.