An buɗe taron tattaunawa kan fasahar AI da dimokuraɗiyya na shekarar 2026, inda aka mayar da hankali kan tasirin fasahar ga zaɓukan Najeriya na 2027.
A jawabinsa na maraba, Babban Daraktan ƙungiyar Yiaga Africa, Samson Itodo, ya jaddada muhimmancin sahihan bayanai, hanyoyin aiki na gaskiya da tsarin fasaha da za a iya tantancewa wajen kare sahihancin zaɓe.
- Mauritius ta sanya dokar hana fita bayan barkewar zanga-zanga
- RMAFC ta buƙaci ma’aikata su ƙara ƙwazo da riƙon amana
A saƙonninsu na fatan alheri wakilan Luminate, Tarayyar Turai da Babban Ofishin Jakadancin Birtaniya, da sauran abokan hulɗa, sun jaddada buƙatar amfani da fasahar cikin kulawa da ɗaukar matakan yaƙi da yaɗa bayanan ƙarya.
Yayin da zaɓukan Najeriya na 2027 ke ƙaratowa, mahalarta taron sun bayyana cewa ci gaban fasaha bai kamata ya tauye sahihancin zaɓe, ko haƙƙin ’yan ƙasa da amincewar jama’a ga tsarin dimokuraɗiyya ba.