Mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Kashim Shettima, ya soki tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar kan matsayinsa game da tallafin man fetur, yana mai cewa sauya akida ba zai magance matsalolin kasafin kuɗin ƙasa ba.

Shettima ya bayyana hakan ne ranar Laraba, yayin ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a zauren liyafa na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya ce Atiku, wanda ya daɗe yana bayyana kansa a matsayin mai goyon bayan tsarin jari-hujja, yanzu ya koma goyon bayan wani tsari da ya yi kama da akidar gurguzu, yana mai kwatanta sauyin matsayinsa da sauya tufafin akida.

Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi tambayoyi kan shirin dawo da tallafin man fetur da Atiku ya gabatar, inda ya ce ya kamata a fayyace wanda zai biya kuɗin shirin, da waɗanda za su amfana da shi da kuma sauran ayyukan gwamnati da za a rage wa kuɗaɗe domin aiwatar da shi.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, ya bayyana cewa zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a shekarar 2027, inda ce tallafin zai mayar da hankali kan samar da man fetur a cikin gida, ba wai tsarin tallafa wa man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje ba.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce shirin zai kasance mai iyaka, a bayyane, cikin kasafin kuɗi kuma ƙarƙashin bincike mai zaman kansa.

A ranar 9 ga Oktoba, ya kuma soki rangwamen farashin man fetur na kwanaki 30 da gwamnatin tarayya ta sanar a gidajen sayar da man NNPC, yana mai cewa bai isa ba kuma ba a bai wa kowa dama iri ɗaya ba.

Sai dai Ministan Kuɗi kuma mai kula da tattalin arzikin ƙasa, Taiwo Oyedele, ya ce rangwamen ba tallafi ba ne, sayar da man fetur ne a kan farashin da aka samar da shi, tare da ba wa masu jigilar fasinjoji fifiko.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *