Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bai wa jam’iyyun siyasa wa’adin zuwa ranar 24 ga Oktoba, 2026, su sanar da ita idan sun gano an cire sunayen ’yan takararsu ba bisa ƙa’ida ba daga jerin ’yan takarar gwamnan jihohi na zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinan INEC kuma Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Masu Zaɓe, Mohammed Haruna, ya fitar a ranar Talata, hukumar ta ce wa’adin ya yi daidai da sashe na 32(2) na Dokar Zaɓe ta 2026, wanda ya tanadi kwanaki 14 domin jam’iyyu su sanar da hukumar game da irin waɗannan kura-kurai.
Daga cikin ’yan takarar da ba a saka sunayensu cikin jerin ba akwai Oladipupo Adebutu na PDP a jihar Ogun da Isa Ali Pantami na PDP a jihar Gombe. Haka kuma, an cire Aminu Gwarzo, ɗan takarar gwamna na Nigeria Democratic Congress (NDC) a Kano, yayin da ADC a Jigawa ta nuna rashin amincewa da cire sunan Aminu Ringim, wanda jam’iyyar ta amince ya zama mataimakin ɗan takarar gwamna, da wasu ’yan takara.
- ADC-PCC ta soki ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen APC
- Mai bincike ya zargi El-Rufai da ware dala 600,000 domin biyan jami’an EFCC
- NSCIA ta taya CAN murnar cika shekara 50 da kafuwa
INEC ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan hukuncin Kotun Ƙoli na ranar 24 ga Satumba, 2026, a shari’ar da ta shafi hukumar da jam’iyyar Zenith Labour Party. Kotun ta tabbatar da cewa tanade-tanaden dokar zaɓe kan rajistar mambobin jam’iyyu da zaɓen ’yan takara wajibi ne, kuma jam’iyyun da ba su bi ƙa’idojin ba ba za su cancanci tsayar da ’yan takara ba.
Hukumar ta ce ta yi amfani da wannan hukunci wajen kammala jerin sunayen ’yan takarar gwamna, tare da jaddada cewa wajibi ne hukumomi su aiwatar da hukuncin kotu. Ta kuma ce jerin sunayen ’yan takarar shugaban ƙasa da na Majalisar Dokoki ta Ƙasa an wallafa su ne tun ranar 12 ga Satumba, kafin hukuncin Kotun Ƙoli.
INEC ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa za ta ci gaba da bin ƙa’idojin doka da tabbatar da gaskiya a tsarin zaɓe, yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan cire sunayen wasu ’yan takara gabanin zaɓukan gwamnonin jihohi da aka tsara gudanarwa a ranar 6 ga Fabrairu, 2027.