Rundunar ’yan sandan jihar Neja ta ce ta kama wani mutum mai shekaru 25 da ake zargi da haɗin baki, kisan kai da satar babur, tare da kwato babur ɗin da aka sace.
A cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Wasiu Abiodun, ya fitar a ranar 14 ga Oktoba, 2026, ya ce an kama wanda ake zargin a ranar 1 ga Oktoba a yankin Gusasse da ke ƙaramar hukumar Bosso.
- Masana sun bukaci a yi amfani da fasaha AI cikin gaskiya wajen zaɓen 2027
- INEC ta ce fasahar AI ba ita ce za ta yanke sakamakon zaɓen 2027 ba
Sanarwar ta ce bincike ya nuna cewa a ranar 30 ga Satumba, wanda ake zargin ya ɗauki hayar wani mai shekaru 23, direban babur mai kasuwanci, domin ya kai shi daga Beji zuwa ƙauyen Garatu.
A kan hanyar dawowa, da misalin tsakar dare, an kai wa direban hari a hanyar Gidan-Kwano zuwa Maikunkele, inda aka fille kansa tare da sace sabon babur ɗinsa.
’Yan sandan sun ce wanda ake zargin ya amsa hannu a laifin yayin tambayoyi, kuma an kwato babur ɗin da adda daga hannunsa.
Ana ci gaba da neman wasu mutum biyu da ake zargi da hannu a lamarin, waɗanda suka tsere.