Kotun ta ce Jonathan zai iya tsayawa takrara shugaban kasa a zaben 2027

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ce tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, yana da damar tsayawa takara a zaben shugaban kasa na shekarar 2027.

Alkalin kotun Mai Shari’a Peter Lifu, ya yi watsi da karar da aka shigar ta neman hana Goodluck Jonathan tsayawa takara a Babban Zaben Shugaban Kasa na 2027.

Alkalin ya bayyana cewa Jonathan ya cancanci tsayawa takara bisa la’akari da wasu hukunce hukunce da Babbar Kotun Tarayya dake Yenagoa, da kuma Kotun Daukaka Kara suka yanke akan wannan batu a baya.

Sakamakon haka, kotun ta ci tarar mai shigar da karar kudi har naira Miliyan Ashirin saboda bata mata lokaci.

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta shiga sahun waɗanda ake ƙara, ta halarci zaman kotun domin shaida yadda aka yanke wannan hukunci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *