Najeriya na ƙara mayar da hankali kan yadda za ta samu ƙarin kuɗaɗe da zuba jari domin inganta hasashen yanayi da tsarin gargadin jama’a kafin faruwar ambaliya, ko fari da sauran bala’o’in da suka shafi yanayi.
Wannan na daga cikin batutuwan da aka tattauna a wani babban taron Ƙungiyar Kula da Yanayi ta Duniya, WMO, a Beijing da Fujian na ƙasar Sin, wanda Darakta-Janar na NiMet, Farfesa Charles Anosike, ya halarta.
- Tinubu ya tsawaita hutun aiki har zuwa karshen mako
- Wike zai bayyana dalilin adawa da Rainbow Coalition
Taron ya tattauna yadda za a haɗa bayanan kimiyyar yanayi da kuɗaɗen sauyin yanayi, tare da amfani da sabbin fasahohi wajen tabbatar da cewa gargadi ya isa ga mutanen da ke cikin haɗari cikin lokaci.
Mahalarta taron sun kuma duba tsarin ƙasar Sin na amfani da basirar wucin gadi wajen hasashen haɗurran yanayi da aika gargadi, a wani mataki na rage asarar rayuka da dukiya.
Ga Najeriya, babban ƙalubalen yanzu shi ne yadda za a mayar da bayanan hasashen yanayi zuwa matakan kariya tun kafin bala’i ya faru, musamman ga manoma da al’ummomin da ke zaune a wuraren da ambaliya da sauran haɗurran yanayi suka fi shafa.