Shugaban Ghana, John Dramani Mahama, ya yi kira ga ƙasashen Global South da su ƙarfafa ƙarfin tattalin arzikinsu na cikin gida, da  inganta hukumomi da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen ci gaba mai ɗorewa, yayin da suke fuskantar ƙarin matsin basussuka da sauye-sauye a tsarin ci gaban duniya.

Mahama ya yi wannan kiran ne a wani taron shugabannin ƙasashe da Gidauniyar Open Society ta shirya a birnin New York, a gabanin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81.

Global South sun ƙunshi  ƙasashe masu tasowa da ke fuskantar manyan ƙalubalen tattalin arziki da ci gaba, musamman a Afirka, da Asiya, da Latin Amurka da wasu ƙasashen Caribbean da Pacific.

Daga ƙasashe akwai Najeriya da Ghana da Kenya da Afirka ta Kudu da Indiya da Indonesia da Brazil da Mexico.

Mahama ya ce ƙasashen na fuskantar ƙarin matsin bashi da kuma sauye-sauye a tsarin tallafin ci gaba na ƙasa da ƙasa, lamarin da ke buƙatar su ƙarfafa hukumominsu da samar da hanyoyin samun kuɗaɗen ci gaba mai ɗorewa.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *