Faransa ta yaba da ƙoƙarin Pakistan na shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka, yayin da Islamabad ke ci gaba da isar da saƙonni tsakanin ƙasashen biyu domin ganin an samu hanyar tattaunawa.

Ministan Harkokin Wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya gana da takwaransa na Pakistan, Ishaq Dar, a gabanin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke gudana a birnin New York.

Barrot ya jaddada buƙatar gudanar da tattaunawa mai faɗi da za ta haɗa dukkan ɓangarorin da abin ya shafa, domin taimakawa wajen tabbatar da wadatar makamashi da kuma magance barazanar da Faransa ke cewa Iran na haifarwa a fannonin makamashin nukiliya da makamai masu linzami da kuma al’amuran yankin.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Faransa ta ce irin wannan tattaunawa na da muhimmanci wajen samar da mafita mai ɗorewa ga rikicin da ke tsakanin Iran da Amurka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *