Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutane 11 da wasu ’yan bindiga suka yi ƙoƙarin sacewa a kan hanyar Kabba zuwa Ayere, da ke Ƙaramar Hukumar Kabba-Bunu a Jihar Kogi.
Wata sanarwa da mai magana da yawun Birged ta 12 ta Sojin Najeriya, Laftanar Hassan Abdullahi, ya fitar ranar Litinin, ta ce lamarin ya faru ne ranar 18 ga Oktoba, 2026.
Sanarwar ta ce sojojin da ke gudanar da sintiri sun samu bayanan sirri kan wasu ’yan bindiga da ke ƙoƙarin sace fasinjojin wata motar haya. Bayan isa wurin, sojojin sun yi arangama da maharan, inda suka tsere zuwa daji suka bar fasinjojin.
- Rikicin zanga-zanga a Faransa ya tayar da muhawara kan baƙin haure a Kasar
- Shugaban Zambia ya bukaci a mayar da hankali kan hana rikice-rikice ta hanyar bunƙasa tattalin arziki
An kuɓutar da mutane tara, ciki har da direban motar, sai dai direban da wasu fasinjoji biyu sun samu raunuka, kuma an kai su asibiti domin kula da lafiyarsu.
A ranar 19 ga Oktoba, sojojin sun sake bincika yankin, inda suka gano wasu fasinjoji biyu da suka gudu zuwa daji a lokacin arangamar. Hakan ya sa adadin mutanen da aka kuɓutar ya kai 11.
Rundunar Sojin Najeriya ta buƙaci jama’a da su riƙa kai rahotannin da suka shafi tsaro ga hukumomi cikin gaggawa domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan tsaro.