Haɗadɗiyar Daular Larabawa ta dakatar da dukkan zirga-zirgar jiragen saman da kamfanonin Iran ke yi zuwa ƙasar, ana ganin matakin yana da alaƙa da takunkumin da Amurka ta ƙakƙaɓa wa ɓangaren sufurin jiragen saman Iran.

Matakin ya sanya Hadaddiyar Daular Larabawa cikin jerin ƙasashe irin su Oman da Iraqi da Azerbaijan da Jojiya da Turkmenistan da suka dakatar da zirga-zirgar jiragen Iran.

Dubai, wadda ke cikin manyan cibiyoyin kasuwancin yankin, na daga cikin muhimman wuraren da kamfanonin jiragen Iran ke yawan zuwa, saboda yawan zirga-zirga da kuma alaƙar kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an soke wani jirgin Iran Airtour da zai tashi daga Tehran zuwa Dubai a safiyar Alhamis, bayan an riga an sayar da tikitin fasinjojin.

Hakan na zuwa ne bayan Hadaddiyar Daular Larabawa ta ce ta dakatar da wasu harkokin kasuwanci da na kuɗi da Iran a watan da ya gabata.

A ranar Laraba kuma, babban bankin Hadaddiyar Daular Larabawa ya dakatar da wasu hada-hadar kuɗi da Bank Melli na Iran, yana zargin bankin da karya ƙa’idojin da suka shafi safarar kuɗaɗen gyabu, da safarar makamai.

A farkon watan nan, Amurka ta sanar da sabbin takunkumai masu yawa kan ɓangaren sufurin jiragen saman Iran, inda ta sanya takunkumi kan kamfanonin jiragen sama 27 da wasu kamfanoni da ke tallafa musu.

Amurka ta yi gargadin cewa filin jirgin sama ko kamfanin da ya ci gaba da yi wa kamfanonin Iran hidima na iya fuskantar matsalar samun damar amfani da tsarin dalar Amurka.

A gefe guda, mai magana da yawun Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Iran, Majid Akhavan, ya ce ana ci gaba da tattaunawar diflomasiyya da ta harkokin sufurin jiragen sama domin cire takunkumin da kuma dawo da zirga-zirgar jirage zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa.

Ya kuma tabbatar da cewa Turkmenistan ta mayar da wani jirgin da ya taso daga Tehran zuwa Dushanbe bayan ta hana shi wucewa ta sararin samaniyarta. Duk da haka, wasu ƙananan kamfanonin jiragen Iran na ci gaba da zirga-zirga zuwa China da Armenia, yayin da wasu jirage zuwa Turkiyya kuma ke ci gaba da aiki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *