Gwamnatin Najeriya ta sake jaddada aniyarta ta rage gibin rayuwa da ke tsakanin masu fama da cutar sikila, tare da haɗa gwiwa da wasu ƙasashe da ƙungiyoyin duniya wajen ƙaddamar da sabon shiri na inganta kula da masu cutar.
Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a na Jiha, Dakta Iziaq Adekunle Salako, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a a wajen ƙaddamar da shirin Global Partnership to Advance Equity and Transform Sickle Cell Care, da aka gudanar a Majalisar Ɗinkin Duniya da ke New York, a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya na UNGA 81.
Najeriya ce ta shirya taron tare da Uganda, Indiya, Jamaica da Saint Kitts and Nevis, da kuma UNICEF, WHO, Africa CDC, Asibitin Binciken Yara na St Jude da World Coalition on SCD. Dakta Salako ya ce kusan mutane miliyan takwas ne ke fama da cutar sikila a duniya, yayin da sama da kashi 75 cikin 100 ke zaune a yankin Afirka kudu da Sahara.
Ya ce Najeriya ce ƙasar da cutar ta fi addaba a duniya, inda ake samun jarirai tsakanin 150,000 zuwa 180,000 da aka haifa da cutar a duk shekara.
Ya ce hakan ya sanya cutar sikila cikin abubuwan da gwamnati ke bai wa muhimmanci wajen rage mace-macen yara da mata da kuma inganta kiwon lafiya.
Ministan ya ce gwamnati ta ƙarfafa shirinta na yaƙi da cutar ta hanyar kafa wani shiri na ƙasa a ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya, da kwamitin kula da shirin da kuma ƙa’idojin kula da masu cutar.
Ya ce ana gudanar da gwaje-gwajen gano cutar tun bayan haihuwa a Legas, Kano da Abuja, yayin da aka kafa cibiyoyi shida na musamman da ke da na’urorin HPLC domin gano cutar yadda ya kamata.
Dakta Salako ya ce rashin daidaito da ƙarancin fifiko ga cutar a duniya na daga cikin matsalolin da suka hana samun ingantacciyar kulawa, musamman kasancewar yawancin masu cutar na cikin ƙasashe masu ƙarancin kuɗi da matsakaicin kuɗi.
Ya ce Najeriya, a matsayinta na ƙasar da ke jagorantar shirin OneSCD, za ta mayar da hankali kan gano cutar da wuri da cikakkiyar kulawa, tare da sanya marasa lafiya da iyalansu a tsakiyar manufofi, sannan ta yi kira ga ƙungiyoyin ci gaba, masu bayar da tallafi da kamfanoni masu zaman kansu da su zuba jari wajen faɗaɗa hanyoyin magance cutar da suka tabbatar da tasiri.