Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta sake jaddada cewa ba ta goyon bayan kowace jam’iyya ko ɗan takara a zaɓen 2027.
INEC ta ce abin da take da shi kawai shi ne kare muradun al’ummar Najeriya.
- Shettima ya buƙaci sabuwar jagorancin ECOWAS ta fifita haɗin kan ƙasashen yammacin Afirka
- Najeriya ta doke Madagascar a wasan farko na neman gurbin Gasar AFCON ta 2027
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya bayyana hakan yayin ziyararsa ga Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, a Kaduna, inda ya ce INEC za ta kasance mai tsaka-tsaki, da adalci da gaskiya a harkar zaɓe.
Ya ce, “Ba mu da ’yan takara, ba mu da jam’iyya, ba mu da wata maslaha face ikon zaɓin al’ummar Najeriya.”
Ya ƙara da cewa hukumar ta fara shirye-shiryen zaɓen 2027 tun da wuri, domin tabbatar da cewa tsarin zaɓen ya kasance cikin tsari da kuma sahihanci.