Super Eagles ta Najeriya ta fara yaƙin neman tikitin shiga Gasar Cin Kofin nahiyar Afirka ta 2027 da nasara mai ban wahala, yayin da ta doke Barea ta Madagascar da ci 2-1 a wasan da suka buga ranar Jumma’a, a filin wasa na Godswill Akpabio dake Uyo.
Barea ta girgiza Super Eagles, inda ta fara zura mata ƙwallo a minti na 16 ba zato ba tsammani.
Madagascar ta riƙe nasarar har zuwa daf da tafiya hutun rabin lokaci inda sabon ɗan wasan Super Eagles, George Ilekhiena, ya farke wa Najeriya ƙwallon da aka zura mata.
-
Tsohon kyaftin ɗin Super Eagles, Troost-Ekong, ya karɓi Musulunci a Qatar
-
NPFL: Barau FC ta ci gaba da samun nasara, yayin da Enyimba ta sha kashi a gida
-
Babu tashin hankali tsakanina da Dembele kan maganganun Ballon d’Or – Mbappe
Super Eagles ta ci gaba da mamaye wasan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci tare da kai hare-hare.
Koci Eric Chelle ya sake saka wani sabon ɗan wasa, Moses Usor, wanda ya canza akalan wasan ya zura wani ƙwallo mai ban sha’awa cikin nutsuwa da gwarin gwiwa.
Madagascar ta yi ƙoƙarin daidaita wasan a ƙarshe, amma Super Eagles ba ta bata damar yin hakan ba don samun maki uku gaba ɗaya da kuma buɗe yaƙin neman shiga Gasar AFCON ta 2027 da nasara.
Najeriya za ta koma fagen fafatawa a ranar 29 ga Satumba yayin da za ta kara da Guinea-Bissau a wasa na biyu na rukunin L.
