Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci sabuwar jagorancin Hukumar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka, ECOWAS, da ta mayar da haɗin kan yankin da haɗa kan al’ummomi cikin manyan abubuwan da za su sa a gaba.

Shettima ya bayyana hakan ne a New York, Amurka, yayin da ya karɓi tawagar sabuwar jagorancin ECOWAS ƙarƙashin jagorancin sabon Shugaban Hukumar, Janar Birame Diop mai ritaya, a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 81.

Ya ce ECOWAS na buƙatar ƙarin haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin, musamman wajen samar da manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar jama’a da tattalin arziƙin yankin.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma buƙaci hukumar ta ƙara ƙoƙarin gina kyakkyawar alaƙa tsakanin ƙasashen yammacin Afirka, tare da yin hulɗa da sabbin ƙungiyoyin yankin ciki har da ƙungiyar Alliance of Sahel States, AES.

Haka kuma, Shettima ya jaddada muhimmancin shigar kamfanoni masu zaman kansu cikin aikin titin Lagos zuwa Abidjan, wanda ake kallonsa a matsayin wani muhimmin aikin haɗa harkokin kasuwanci da zirga-zirga tsakanin ƙasashen yankin.

A nasa jawabin, sabon Shugaban Hukumar ECOWAS, Janar Birame Diop, ya yaba da irin rawar da Najeriya ta taka wajen kafa da kuma dorewar ƙungiyar, tare da neman ƙarin haɗin gwiwar Najeriya wajen tunkarar matsalolin tsaro da ci gaban tattalin arziƙin yankin.

Ya ce ECOWAS na fuskantar ƙalubale da dama da suka haɗa da matsalar tsaro da rashin isasshen ci gaba, lamarin da ya ce ke buƙatar haɗin kan shugabannin ƙasashen yankin.

A yayin ganawar, Shettima ya tabbatar wa sabon shugaban ECOWAS cewa Najeriya za ta ci gaba da ba hukumar haɗin kai da goyon baya wajen cimma manufofinta na inganta zaman lafiya, haɗin kan yankin da ci gaban tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *