Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce ci gaba da hana Afirka samun kujerar dindindin a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya na raunana adalci da sahihancin tsarin mulkin duniya.
Shettima ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Hajiya Amina Mohammed, a gefen taron babban zauren Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 da aka gudana a New York.
Ya ce Najeriya na goyon bayan sake fasalin Majalisar Ɗinkin Duniya domin tabbatar da cewa cibiyoyin duniya sun fi wakiltar yanayin siyasa da yawan al’ummar duniya na ƙarni na 21.
- Ba mu da ɗan takara, ba mu da jam’iyya a zaɓen 2027 – INEC
- Najeriya da Jamus sun ƙarfafa haɗin gwiwa domin haɓaka masana’antar ƙarfe
Mataimakin Shugaban Ƙasar ya kuma yaba wa Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, António Guterres, kan matsayinsa na neman samar da Kwamitin Tsaro da zai fi wakiltar duniya, yana mai cewa rashin wakilcin Afirka na dindindin a kwamitin bai dace da tsarin duniya na yau ba.
Wannan matsaya ta Shettima na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan ya gabatar da matsayin Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya, inda Najeriya ta nemi a bai wa Afirka aƙalla kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro, tare da cikakken ikon veto muddin wannan tsarin na veto ya ci gaba da kasancewa.
Najeriya ta kuma nemi kujeru biyar na wucin gadi ga nahiyar Afirka.
Shettima ya ce Najeriya za ta ci gaba da kasancewa abokiyar hulɗa wajen sake gina amincewa tsakanin ƙasashe, kare dokokin ƙasa da ƙasa da kuma tunkarar matsalolin yunwa da rikice-rikice da wariya.
Ya kuma jaddada cewa amincin tsarin duniya zai dogara ne da yadda yake magance wahalhalun bil’adama cikin adalci tare da bai wa dukkan yankuna damar taka muhimmiyar rawa wajen yanke shawarar da ta shafi duniya baki ɗaya.