Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya yi kira ga ’yan siyasa, da ’yan takara da magoya bayansu da su guji tashin hankali da kalaman ƙiyayya yayin da ake shirin babban zaɓen 2027.
Shugaban hukumar ya yi wannan kiran ne yayin wata ziyara ga Sarkin Zazzau, inda ya ce zaɓe ya kamata ya zama hanyar da ’yan Najeriya ke bayyana ra’ayinsu cikin lumana, ba wani lamari da za a mayar da shi “batun rai ko mutuwa” ba.
- Bai kamata a ci gaba da ware Afirka daga kujerar dindindin ta Kwamitin Tsaro ba – Shettima
- Ba mu da ɗan takara, ba mu da jam’iyya a zaɓen 2027 – INEC
Ya kuma roƙi sarakunan gargajiya da su yi amfani da tasirinsu wajen jan kunnen matasa kan kada su bari ’yan siyasa su yi amfani da su wajen aikata rikicin siyasa.
INEC ta ce tana ƙarfafa haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa zaɓen 2027 ya gudana cikin lumana da amincewar jama’a.