Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, ta ce ta sauya salon shirye-shiryenta domin kauce wa yin ayyukan shirya zaɓe a cikin gaggawa yayin da babban zaɓen 2027 ke ƙara kusantowa.
Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, SAN, ya ce INEC ta fara gwaji, da bincike da ƙarfafa tsarin aikinta tun da wuri, saboda girma da kuma sarkakiyar gudanar da zaɓe a Najeriya.
- Ba mu da ɗan takara, ba mu da jam’iyya a zaɓen 2027 – INEC
- Zaɓe ba batun ko a yi rai ko mutuwa ba ne – INEC ta gargaɗi ’yan siyasa
Ya bayyana cewa hukumar tana aiki da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki domin ƙara fahimtar bukatun jama’a da kuma gina amincewa da tsarin zaɓe.
Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, ya kuma buƙaci INEC ta tabbatar da cewa kayan zaɓe da na’urorin da za a yi amfani da su sun isa wuraren zaɓe a kan lokaci kuma an gwada su sosai kafin ranar zaɓe.