Rundunar ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta ce ta fara neman direban wata mota kirar Toyota 4Runner da ake zargi ya haddasa fashewar wata masana’antar sayar da iskar gas a yankin Byazhin da ke Kubwa.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar Lahadi a Liberty Junction, inda motar da ke tafiya ba bisa ka’ida ba a hanya mai hanya ɗaya ta rasa kwacewa direban, ta kutsa cikin masana’antar gas tare da haddasa tashin gobara mai ƙarfi.
’Yan sanda daga sashen Kubwa sun isa wurin tare da tuntuɓar Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, wadda ta taimaka wajen shawo kan gobarar da ta bazu zuwa wasu shaguna da kadarorin da ke kusa.
- INEC ta ce za ta fara shirye-shiryen zaɓen 2027 tun da wuri
- Zaɓe ba batun ko a yi rai ko mutuwa ba ne – INEC ta gargaɗi ’yan siyasa
A cewar ’yan sandan, direban da sauran mutanen da ke cikin motar sun tsere daga wurin bayan hatsarin.
Rundunar ta ce ta riga ta gano wanda ake nema, kuma tana ci gaba da farautarsa domin yi masa tambayoyi da gudanar da bincike.
Sai dai rundunar ta tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba, yayin da har yanzu ba a kammala tantance yawan asarar dukiyoyin da gobarar ta haifar ba.
Rundunar ta kuma ce an dawo da zaman lafiya a yankin, inda ta bukaci mazauna wurin su ci gaba da kasuwancinsu bisa doka.