Kamfanin NNPC ya ce,  ya samu ribar bayan haraji ta Naira tiriliyan 7.2 a shekarar 2025, wanda ke nuna ƙarin kashi 33 cikin 100 idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 5.4 da ya samu a shekarar 2024.

Kamfanin ya bayyana hakan ne yayin gabatar da sakamakon binciken kuɗaɗensa na shekarar da ta ƙare a ranar 31 ga Disamba 2025.

Jimillar kuɗaɗen shigar kamfanin ta kai Naira tiriliyan 34.5, yayin da ribar da aka ware wa masu hannun jari ta ƙaru da kashi 35 zuwa Naira tiriliyan 5.8.

A bangaren samar da man fetur, NNPC ta ce matsakaicin abin da Najeriya ta samar daga danyen mai ya kai ganga miliyan 1.77 a kowace rana a 2025, matakin da kamfanin ya ce shi ne mafi yawa cikin shekaru biyar.

Kamfanin ya kuma bayyana cewa ya kammala manyan ayyuka da dama da suka haɗa da babban layin iskar gas na Ajaokuta zuwa Kaduna zuwa Kano mai tsawon kilomita 623, tare da ci gaba da ayyukan samar da iskar gas da sauran ababen more rayuwa a bangaren makamashi.

Shugaban Kamfanin NNPC, Injiniya Bashir Bayo Ojulari, ya ce sakamakon shekarar 2025 ya nuna abin da za a iya samu ta hanyar ingantaccen gudanarwa, da ƙara samar da man fetur da kuma saka jari a ma’aikata da kadarorin kamfanin.

NNPC ta kuma ce tana da burin ƙara samar da danyen mai zuwa ganga miliyan biyu a kowace rana nan da shekarar 2027, sannan ganga miliyan uku a kowace rana zuwa 2030.

Kamfanin ya kuma bayyana shirin jawo jarin dala biliyan 60 a bangarorin man fetur da iskar gas zuwa shekarar 2030.

By Bashar Muhammad Dange

Bashar Muhammad is a Nigerian multimedia journalist, broadcaster, producer, and media professional with years of experience in radio broadcasting, reporting, and content creation. He holds a B.Sc. in Mass Communication from Ahmadu Bello University, Zaria, and a Diploma in Mass Communication from The Polytechnic of Sokoto. Throughout his career, Bashar has produced and presented programmes on current affairs, agriculture, health, education, and community development. He has worked with leading media organizations including Garkuwa FM 95.5 Sokoto, Trimming Radio 96.5 FM Goronyo, Giantability Media Network, and ABU Samaru FM. As a journalist and presenter, he has conducted interviews, reported on social and developmental issues, and amplified the voices of underserved communities. Beyond broadcasting, Bashar has demonstrated leadership in media management, programme development, and team coordination. He has received several awards and recognitions for his contributions to journalism, Hausa language development, and community service. His expertise includes radio production, news reporting, sound editing, investigative journalism, media analysis, and public presentation. Driven by a passion for impactful storytelling and public service, Bashar Muhammad continues to use journalism and media platforms to inform, educate, and empower communities across Nigeria.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *