Shugaban ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) na ƙasa, Sheikh Dr. Abdullahi Bala Lau, ya jaddada cewa amfani da ƙarfin soji kaɗai ba zai iya zama cikakkiyar mafita wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Najeriya ba.
Yayin da yake magana a shirin Babbar Majalisa na Manara TV, Sheikh Bala Lau ya ce tattaunawa, da ilimantarwa da wayar da kan jama’a na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalolin tsaro da sauran ƙalubalen da ƙasar ke fuskanta.
Bala Lau bayyana cewa shugabannin addinai, da shugabannin al’umma da ɗaiɗaikun jama’a duk suna da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai.
Ya kuma jaddada cewa bambance-bambancen addini, ko kabila ko yanki bai kamata ya zama abin da zai hana haɗin kai da ci gaban Najeriya ba.
Sheikh Bala Lau ya kuma yaba da babban taron ƙasa da ƙasa kan tsaro da ci gaban ƙasa da JIBWIS ta gudanar tare da haɗin gwiwar Muslim World League (MWL) a Abuja, yana mai cewa taron ya samar da damar fahimtar juna da ƙara haɗin gwiwa tsakanin malaman Musulmi da Kiristoci wajen neman hanyoyin gina Najeriya mai zaman lafiya.
Dangane da siyasa da mulki, Sheikh Bala Lau ya ce JIBWIS tana bin hanyar nasiha, da shawara da gyara cikin hikima, ba tare da tayar da hankalin jama’a ko shiga gaba da gwamnati ba.
Ya ƙara da cewa malamai na da damar ba da shawara, amma ba za su tilasta wa mutane wanda za su zaɓa ba.
Ya yi kira ga kowane ɗan ƙasa da ya fahimci cewa tabbatar da zaman lafiya da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyansa, tare da yin aiki tare domin haɗin kai da ci gaban Najeriya.