Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ’yan Najeriya masu shekaru 15 zuwa 35 da su yi rajista a Bankin Bayanai na Matasa na Ƙasa (NYDB), domin taimakawa wajen gano ƙwarewarsu, da bukatunsu da kuma wuraren da suke zaune.

Gwamnatin ta ce bayanan za su taimaka wajen haɗa matasan da damarmaki a hukumomin gwamnati da kuma kamfanoni masu zaman kansu.

Ministan Matasa, Comrade Ayodele Olawande, ne ya yi kiran a ranar Talata a Abuja, yayin ƙaddamar da shirin Bankin Bayanai na Matasa na Ƙasa.

Olawande ya ce rajistar za ta shafi matasan da ke aiki a ɓangaren gwamnati da kuma waɗanda ke sana’o’in kansu, ciki har da masu aikin noma, da wasanni, da masana’antun ƙirƙire-ƙirƙire da fasahar zamani.

Ya ce samun sahihan bayanai kan matasan Najeriya zai taimaka wa gwamnati wajen rage tazarar da ke tsakaninta da matasa, tare da inganta tsare-tsare da aiwatar da shirye-shiryen da suka shafi matasa.

Ministan ya ce bayanan za su taimaka wajen amsa muhimman tambayoyi kamar su: “Su waye matasanmu?”, “Ina suke?”, “Me za su iya yi?” da kuma “Wane irin dama suke bukata?”

Ya kuma bayyana cewa shirin na daga cikin ayyukan gwamnati na dindindin, kuma ba a ƙirƙire shi domin wasu manufofin zaɓe ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *